Share Your Post Fb Group.

Home » category 1 » KARATU DA ILIMI GAMEDA BIOGASS. yadda zaka samar da gas daga kashin shanu dana doki

Share|

KARATU DA ILIMI GAMEDA BIOGASS. yadda zaka samar da gas daga kashin shanu dana doki

MENENE BIOGAS (BIOMASS) ? Darasi na biyu KARATU DA ILIMI GAMEDA BIOGASS. yadda zaka samar da gas daga kashin shanu dana doki _____________ A ranar 30 June munfara bayani akan BIOGAS , ban shiga bayani kai tsaye ba har saida na fara bada labarin abinda yafaru dani gameda iskar kunun ayar Dana aje a daki na. Yau kuma zamu shiga cikin karatu batareda bata lokaci ba insha Allahu Rabbi, ina fatan dai masu bibiyan rubutu na basu manta labarin Dana basu ba. Daga farko dai idan mai karatu ya dubi Kalmar BIOGAS zaiga kamar tana dauke da kalmomi guda biyu wato "Bio" da kuma "gas". Kalmar "bio" mutane sunfi saninta a cikin Kalmar biology, biochemistry, biography. Kalmar bio asalin Kalmar ba English bace, Kalmar Greek ce, idan akace bio a yaren mutanen Greek to ana nufin "life" wato rayuwa ko Abu mai rai. Kalmar "gas" yana nufin Air a turance, a hausa kuma iska kenan. Idan kahada kalmomin guda biyu zaibaka "BIOGAS" Wanda hakan yana nufin "rayuwar iska" ko kuma "iskar dake cikin Abu mai rai". Ya kai mai karatu inaso kasani cewa, mutane da dabbobi da kuma tsirrai wato plants dukkan su living organisms ne a turance. Yayin da ka sanya kunun aya acikin gora komi kashin Sa (ina nufin Dan kadan acikin gorar), ita Kanta ayar plant ce don haka tanada rai, idan kunun aya yakwana acikin gora , enzymes zasu fara hayayyafa acikin Sa Wanda hakan zaisa yafara lalacewa harma ya ru6e saboda iska baya shigan Sa , wannan Ru6ewan da kunun ayar keyi shi ake Kira da turanci anaerobic (anairobik) digestion. Yayin da yake rubewan iskar methane gas (CH4) yana fita daga cikin kunun ayar, idan babu inda iskar zai fita daga cikin gorar (ma',ana idan ka rufe gorar da murfi) to babu inda iskar zai fita. Hakan zaisa iskar yayita taruwa acikin gorar. Shi wannan iskar yana iya kamawa da wuta kamar yadda iskar gas cooker ke kamawa da wuta. Dayawan kasashen turawa da kasar India dasu Pakistan sundade da fara amfani da iskar biogas (BIOMASS) wajen girki domin yafi sauki kuma yafi rashin hatsari sosai. Baya jawo gobara irin yadda cylinder gas yake yi. Nasan mutane zasu so suji ko shin meyasa nace iskar tusa yana iya kamawa da wuta kamar gas cooker? Kabiyoni a karatu na gaba insha Allahu Rabbi. Zamuci gaba . Allah shine mafi sani.
2021 ago [04-07-21 (18:44)]

About Author

admin
author

No responses to KARATU DA ILIMI GAMEDA BIOGASS. yadda zaka samar da gas daga kashin shanu dana doki

    Be first Make a comment.

Leave a Reply

You must be logged in to post a comment.

Categories