A wannan zamani da muke ciki Muminai sun fi kowa bukatar karfafa imaninsu da jaddada shi, saboda yadda karfin Duniya ya nufi shafe imani a bayan kasa. Idan an ce imani a nan, ana nufin shafe duk wani abu mai alaka da Addini - musamman Addinin gaskiya - da mayar da mutane kan Ilhadi.
Kuma akwai hanyoyi masu yawa da ake bi, tun daga kokari shafe banbance banbance tsakanin Addinai, da kuma yada sharholiya, ta hanyar yada kide-kide da wakoki da wasanni, da buude gidajen rawa da sauran wuraren sharholiya, masu haifar da munafurci a cikin zuciya da kin Addini da fada da shi.
Sa'annan kuma a bude wa mutane kofofin lalata tarbiyya da watsi da kyawawan dabi'u da halaye na gari, ta hanyar bude kofar kafofin sada zumunta, don kowa ya koyi rashin mutunci a zubar da kimar masu kima a cikin al'umma, saboda dattaku da riko da Addini.
Don haka babbar manufa da aikin mayar da Duniya ta zama kwarya a tafi hanu (globalization), shi ne raba mutane da Addini, a koma rayuwar dabbobi, ba abin da aka sani sai ci da sha da sharholiya.
Don haka ka sani kai mai hankali ne. Hankalinka ya nuna maka cewa; ba kai ka samar da kanka ba, kuma ba zai yiwu a ce an same ka ba tare da wanda ya samar da kai ba. Don haka dole kana da mahalicci.
Haka kuma ka san cewa; hankalinka ya nuna maka cewa; ba zai taba yiwuwa a ce Mahaliccinka ya halicce ka ne a banza babu manufa ba. A'a, dole halittarka ta zama tana manufa, kuma tana da makoma. Saboda ba za a samu sakamako da natita ta manufar samar da kai a Duniya ba dole sai an koma makoma.
Saboda haka Allah shi ne ya halicce ka, kuma akwai manufa game da halittar taka, kuma akwai makoma.
Misali wannan shi ne: kana kwance kana bacci, kawai sai ka farka ka ganka a cikin jirgi. To wadanne tambayoyi ne za su fara zuwa a tunaninka, wadanda za ka tambayi wadanda ka gani a tare da kai?
Tambayoyi ne guda uku:
1- Wa ya kawo ni nan?
2- Me ya sa ya kawo ni?
3- Ina za mu je?
Don haka kamar haka ne, a lokacin da ka tashi ka yi wayo, ka fara fahimtar abubuwa, ka ganka a cikin wannar Duniya, to ya kamata ka san akwai wadannan tambayoyi guda uku, kuma ana bukatar ka san amsarsu.
1- Wa ya halicce ni ya kawo ni Duniya?
2- Me ya sa ya kawo ni Duniya?
3- Ina za mu je bayan Duniya?
Saboda haka mai hankali sai ya ajiye sharholiya, ya tsaya ya yi abin da ya kamata.
No responses to Nasiha Ga Mumini
Be first Make a comment.